bahaushe logo
TUNZURARWA/HABAICI
INA RUWAN WANI DA WANI, WAI MAHAUKACI YAYI BAKO!
GANE MINI HANYA, MAKAHO YA SO GULMA!
DAGA UHM SAI UHM, UWAR GULMA TAYI CIKIN SHEGE!
MUJE ZUWA, MAHAUKACI YA HAU KURA!
TA KWANA GIDAN SAUKI, WAI RUWA TA WA MAI SON WANKA DUKA!
MARA GASKIYA KO A RUWA YAYI JIBI!
KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KARBAN KUDI!
LAIFI TUDU HAU NAKA KA HANGI NA WANI!
ABIN NEMA YA SAMU,WAI ME SON KUKA AN JEFE SHI DA KASHIN AWAKI!
IM BABU RAMI TO ME YA KAWO RAMI!
DAN KUKA SHI KE JA WA UWARSA HARBI!
MUNAFUNCI DODO, YA KAN CI MAI SHI!
IDAN MUTUM YACE ZAI HADIYE GATARI,TO KA SAKAM MAR KOTA!
RUWA CIKIN COKALI YA ISHE MAI HANKALI WANKA!
GARGADI
DUK WANDA YAKI JIN BARI, YA JI HOHO!
IN ANA TA KAI BA'A TA KAYA!
DUK BALAGAR DAN BUNSURU YA KIYAYI MATAN KURA!
KOMAI NESAN JIFA, KASA ZAI KOMO!
ANA TAUNA TSAKUWA NE DON AYA TA JI TSORO!
IN KAJI KI GUDU ,TO TABBAS SA GUDU BAI ZO BA!
WANDA YAKI JI BA ZAI KI GANI BA!
WANDA YAKI SHARAN MASALLACI YAYI NA KASUWA!
HAKURI
MAI RABON GANIN BADI YA GANI!
SARA DA SASSAKA BAYA HANA GAMJI TOFO!
ALBARKACIN KAZA KADANGARE KE SHAN RUWAN KASKO!
KOMAI TSAWON DARE GARI ZAI WAYE!
MAI HAKURI SHI KE DAFA DUTSE YA SHA ROMON SA!
BA'A GINA DAKI A KWANA DAYA!
IN ANYI HAKURI INDA JIRGI YAJE KUNKURU MA ZAI JE!
IYA MAGANA
GABA DA GABANTA, ALJANI YA TAKA WUTA!
KALLO YA KOMA SAMA, WAI SHAHO YA DAU GIWA!
KOMAI NESAN JIFA, KASA ZAI KOMO!
WAIWAYE ADON TAFIYA NE!
TURNUKU FADAN IBILISAI, WAYA GANI BALLE YA RABA!
KUKAN KURCIYA JAWABI NE MAIHANKALI KE GANE WA!
BA'A CINIKIN BIRI A SAMA!
TA FADO DAGA SAMA TA ZARCE RIJIYA!
KO BA'A GWADA BA HANNU DAYA BAI DAUKAR JINKA
A SA A BAKA YAFI A RATAYA, INJI KURA!
A BAKIN TSOHO NE GORO KAN TSUFA!
KIRARI
KAGANGARAN BAKIN TULU KAKI SHIGA KAKI FITA!
MURUCIN KAN DUTSE BAKA FITA SAI KA SHIRA
GWANGWALA! A HAUKA A ZAME KA HAU MUTUM KA ZAUNA DAI-DAI
Shafin gaba
Duk mai son ya koyi gina Website hadaddiya to maza ya hadu da mu a dandalin mu na koyarwa a facebook SHIGA
Ana iya turo mana da sakonni na Comment (Turo) ko ka shiga dakin Muhawara don tambaya, ko korafi (Shiga)
| | | | |
Online counter:  free web counter Counter Powered by  RedCounter
engTranslate This page
Kirkira:
Umar Muhammad Bappa Plateau state. NIGERIA
© Bahaushe 2016

Old school Easter eggs.