bahaushe logo
IYA MAGANA
IKON ALLAH! AKUYA TA CINYE KURA.
ALLAH KADAI YA SAN KARATUN KURMA.
KO NA GOYE YA SAN KURA.
KAINUWA DASHEN ALLAH.
MAI AKUYA YABI DARE BARE MAI KURA.
ABU MAI SAUKI CIRE WANDO TA KAI.
IDAN RAKUMINKA YA BACE HAR CIKIN TANDU KA DUBA.
KU DAI AKE JI, MAHAUKACI YA FADI A RIJIYA.
WANDA KE SON ZUWA SAMA IN YA TAKA LEDA YA RAGE HANYA.
IDAN FARAUTA TA KIKA, KO KUNKURU TSERE MAKA ZAI.
AIKIN BANZA, WAIWAYE CIKIN DUHU.
AIKIN BANZA, KIBA A KUNNE.
BIKIN MAGAJI BAI HANA NA MAGAJIYA.
MARABA GASASSHE, KURA TA GA BAKAR JAKI.
MAI HANKALI SHI KE GANE DINGISHIN KWADO.
A RANAR WANKA BA'A BOYE CIBI
KOWA YAYI RAWA BALLE DAN MAKADI
HABAICI
TAMU TA SAME MU MALAM DA MALAM DA TALLAR JIGIDA.
CIN DANKO HAR DA KAZA.
KARUWA BA TA KIWON KAZA
AN YI WA ROGO GANIN KITSE
NA SAN A RINA WAI AN SACE ZANIN MAHAUKACIYA.
SABON SALO GEMU A KAFADA.
BISHIYA NA YIWA KUNKURU GORIN KAFA.
BA'A BAI WA KURA AJIYAN NAMA.
ABIN RABO NE AUREN MACE DA CIKI.
GANIN GIDA KAREKANZAGI KURA.
RASHIN SANI KAZA TA KWANA KAN DAMI.
UNGULU BA KAZAR KOWA BA CE.
ABIN DUNIYA MENENE KAZA TA JANYO MUZURU KWANAN GIDA.
RABA ARNE DA MAKAMI IBADA.
DAGA BAYA KENAN WAI ANYI SADAKA DA KARUWA.
MASSALACIN KURA BA'A BAI WA KARE LIMANCI.
IDAN KURA NA MAGANIN ZAWO TA YI WA KANTA.
ABU MAI SAUKI KURA TA JE GIDAN MAHARBI.
MAI HANKALI BAI YAWO TSIRARA.
MUN GAJI DA GAFARA SA BAMU GA KAHO BA.
IYA MAGANA
MUSHEN KURA YA WUCE ALLAH SARKI
ABIN DA YA BA KA TSORO, TABBAS WATARAN ZAI BAKA TAUSAYI.
KWAI A BAKA TA FI KAZA A AKURKI.
SABO DA KAZA BA TA HANA YANKA.
A NEMA A SAMU SHINE ARZIKI.
A RASHIN SANI, BAKO YA SHA RUWAN WANKA.
A BAR KAZA CIKIN GASHINTA.
KWALLIYA TA BIYA KUDIN SABULU.
YAUSHE A GARI KARE YAJI KUGIN KURA.
DAN KWAI NA YI WA KAZA DARIYA.
WANDA RUWA KE JA, KO TAKOBI AKA MIKA MASA KAMAWA ZAI YI BARE IGIYA.
A WAI! KAZA TA JI WUKA A WUYA.
A SA A BAKA YAFI A RATAYA IN JI KURA.
A SO UWA A SO 'YA' YANTA.
AYI A GAMA YAFI GOBE A KARASA.
FATARA MAI SA A SAYAR DA KAZAN KWANCI.
Duk mai son ya koyi gina Website hadaddiya to maza ya hadu da mu a dandalin mu na koyarwa a facebook SHIGA
Ana iya turo mana da sakonni na Comment (Turo) ko ka shiga dakin Muhawara don tambaya, ko korafi (Shiga)
| | | | |
Online counter:  free web counter Counter Powered by  RedCounter
engTranslate This page
Kirkira:
Umar Muhammad Bappa Plateau state. NIGERIA
© Bahaushe 2016

Ring ring