Kashe gari da sassafe rundunar su sarki dujalu suka mike suka ci gaba da tafiya, bayan kowa ya kimtsa cikinsa.
Tun da aka fara tafiyar sai sarki dujalu ya lura da cewa yar uwarsa hursiya bata da sukuni.
A duk sa'adda ya dubeta sai ya ga alamomin damuwa cike a fuskarta kawai sai yayi murmushi, domin shi kadai ne ya san abin da ke damunta.
Abin da ya bashi mamaki shi ne, mene ne ya hanata ta baiyana masa abin da ke damunta, ba wani abu bane yake damun hursiya ba face tsananin son jin ci gaban labarin sadauki hantaru.
Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya har tsawon kwana uku. duk sa'adda aka yada zango sai hursiyya ta lallaba sarki dujalu domin ya ci gaba da bata labarin.
Da zarar ta fuskanci abinda take so, sai ya kama gyan-gyadin karya, bisa dole hursiya ta hakura itama ta kwanta har barci ya saceta bata sani ba.
Da yammacin kwana na uku ne wannan runduna ta sarki dujalu ta iso wani katon daji mai ban tsoro wanda ake yiwa lakabi da sauratul auzar.
Duk da tsananin yawan wannan runduna ta aljanu da mutane da kuma gagarumin shirinsu sai da kowa yaji tsoro ya shigeshi,bisa tsintar kansu a cikin dajin Sauratul auzar,sarki Dujalu ne kadai bai girgaza ba.
Shi dai dajin sauratul auzar babu komai a cikinsa face manya-manyan bishiyoyi da manyan duwatsu masu ban mamaki.Babu inda mutum zai je a duniya yaga irinsu, sannan siffofin bishiyoyin da duwatsun ma ababan tsoro ne.Sau tari sai mutum ya ga suna motsi da rangaji tamkar zasu haifar da girgizar kasa.
Daga dajin Sauratul auzar zusa Bahar sufiya tafiya ce ta wata hudu kacal, kuma a cikin dajin Sauratul auzar mutum zai yi ta tafiya ta tsawon wata hudu.
Da isowar su Sarki Dujalu farkon dajin,sai Sarki Dujalu ya bada umarni a tsaya.Nan take kuwa na kan dawakai suka dawakansu, Aljanu dake tafiya a sama kuwa suka saki fuka-fukansu suka sauko kasa.
Nan fa kowa yai ladaf aka yi tsit tamkar babu mai numfashi a wajen.
Sarki Dujalu yai gyaran murya sannan ya ce: "Ya ku jama'ata kuyi sani cewa mun iso dajin Sauratul auzar. Daga nan zuwa tekun bahar sufiya inda takobin saiful LUJARA take tafiyar wata hudu ne kacal. Ku yi sani cewa masifu da bala'in da ke cikin wannan daji sun wuce tunani don haka sai kowa ya gyara damararsa, domin komai zai iya faruwa. Ko shakka bana yi da yawa daga cikinmu zasu iya rasa rayuwarsu a cikin wannan daji.Wadanda duk suka kai izuwa karshen wannan daji a raye a cikin koshin lafiya sun cika jarumai kwarai ababan yabo da jinjina.
Koda gama fadin haka sai Dujalu ya dubi Hursiya ya ce, "komai wuya da tsanani ki tabbatar da cewa a ko yaushe kina tare da ni".
Hursiya ta gyada kai tana mai nuna alamun cewa lallai zata kiyaye.
Nan take sarki Dujalu ya zunguri cikin aljanin dake dauke da su shi da Hursiya,suka fara wucewa kan gaba, sannan kowa yabi bayansu a cikin yanayin tsoro da dari-dari.Sai da aka shafe sa'a guda ana tafiya a cikin dajin ba a hadu da komai ba kuma ba a ga wani mugun abu ba.