A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a cikin daular larabawa an yi wata kasa mai suna darul mahabur
kasar darul mahabur na da matukar girma da fadi, kuma ta kunshi manyan birane fitattu guda uku a cikinta wato duk a karkashin mulkin sarki guda daya wanda ake kira da suna maharaz ibini suleidini.
Birnin Darul mahabur ya bunkasa da karfin arziki , yawan al'umma da kuma kasuwanci har ya zama abin kwatance a ko ina cikin duniya.
Sarki maharaz ya kasance mutum mai tausayi, taimako da jin 'kan talakawansa. Allah ya hore masa arziki mai dumbin yawa gami da kaifin hankali da kuma hasashen gaba. Yana da matar aure guda daya kacal mai suna shalifat, kuma basu sami haihuwa ba sai bayan shekara goma sha daya da yin aure, don haka a yanzu 'yarsu karamar yarinya ce 'yar shekara takwas a duniya wadda ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance ana kiranta da suna mulaifa.
Tun daga lokacin da Allah ya baiwa Sarki Maharaz da Shalifat Mulaifa sai suka dauki soyayyar duniya suka dora akanta ya zamana cewa ko kuda ba sa son su ga ya sauka a kanta.
Tunda Mulaifa ta taso ake tsantseni da ita kuma komai sai dai ayi ma ta koda kuwa shan ruwa ne baza ta dauki kofi ta rike ba sai dai a sa ma ta a baki ta sha. Haka cin abinci sai dai kuyangi su rinka zuba ma ta a baki da cokali har sai ta koshi.
Batun jin dadi dai da hutu, masana sun yi bincike sun tabbatar da cewa a wannan zamani babu wanda ya sami daula da ni'ima tamkar Mulaifa saboda ko shi kansa gidan sauratar na Sarki Maharaz ya isa Aljannar Duniya, an tabbatar da cewa babu Masarautar da ya fita ginuwa da kawatuwa. Saboda tsananin kyawun gimbiya Mulaifa kuwa sai da labarinta ya cika ko ina a duniya aka rinka zuwa daga kasa-kasa domin a ganta. Kai ko da Sarki Maharaz ya ga abin yayi yawa sai ya hana mutane ganinta yasa aka killaceta a wani kayataccen gida da ke cikin gidan sarautar ya sanya muggan matakan tsaro a gidan yadda komai jarumtakar mutum da karfin sihirinsa bai isa ya tsallaka wadannan matakan tsaron ba ya shiga har inda Gimbiya Mulaifa take. In banda barori da kuyanginta babu kowa a cikin gidan kuma babu mai shiga gidan face Sarki Maharaz da mahaifiyarta Shalifat. Tun daga ranar da aka ajiye Mulaifa a cikin wannan gida bata kara fita ko ina ba sai idan shekara tayi.
Sannan Sarki ke fita da ita a ranar da ake bikin karshen shekara na bautar gunkin da suke bautawa mai suna Darbuza.
Shi dai wannan gida wanda aka sanya Gimbiya Mulaifa a cikinsa ya kunshi komai da komai na jin dadin rayuwar duniya. A cikinsa akwai wani katon lambu wanda aka zuba dabbobin daji a cikinsa da tsuntsaye iri-iri, babu kalar da babu. Ba komai ne yasa aka shirya wannan lambu ba sai domin a rayuwar Gimbiya Mulaifa babu abin da take so sama da kallon dabbobi,tsuntsaye da tsirrai. A kullum da yamma sai Mulaifa ta shiga cikin wannan lambu,kuyangi na biye da ita suna take mata baya tana kewayawa. Idan ta gaji da yawo a lambun sai taje ta zauna a wani wuri na musamman inda aka ajiye wadansu kujeru na kasaita da tebura duk na zinare. Zamanta ke da wuya sai akawo ya'yan itatuwa kala-kala a zube a gabanta, sannan akawo abinci da kayan shaye-shaye iri-iri.
Mulaifa ta kasance mai jin kai, izza da mulki, amma kuma hakan bai sa ta zamo azzaluma ba. Duk da cewa ita yarinya ce tana da tausayi, amma fa bata son raini, kuma tana takama da kyawunta da kuma matsayinta don haka kuyanginta da barorinta suke matukar shakkarta kuma suke matukar ladabi da biyayya a gare ta.
Sarki Maharaz yayi imani matuka da gunki Darbuza, kuma shi ne wakilin mutanen kasar gaba daya a wajen gunki Darbuza. Duk wani sihirin tsafi wanda Sarki Mahraz ke takama da shi a wajen Darbuza yake samu, kuma duk abin da ya sa a gabansa in dai ya nemi taimakon Darbuza sai ya samu nasara, bai taba samun akasi ba. Bisa wannan dalili ne gaba daya bokayen dake nahiyar suke adawa da shi domin a kullum basu da burin da yafi su ga bayansa kuma su mallaki duk sihirin da yake takama da shi.
Baya ga bokaye, suma dukkanin sarakunan dake nahiyar suna adawa da Sarki Maharaz saboda shi ne ubansu a bangaren karfin mulki da girman kasa. Kowanne sarki burinsa ace yau an wayi gari yafi Sarki Mahraz daukaka da suna amma duk sun makara domin na gaba ya yi gaba na baya sai labari.
Haka kuma a bangaren attajirai Sarki Maharaz ya yiwa dukkan attajiran nahiyar fintinkau, domin babu mai rabin dukiyarsa. Shi dai Sarki Maharaz ya zamo tauraron zamani domin duk abin da ya taba take yake zama kudi, sabo da tsabar yawan darhamin da ya tara sai da aka rasa inda za'a rinka ajiye wa
Dole aka rinka haka rijiyoyi masu zurfin gaba dubu ana cikasu da darhami ana kullewa.
Tun ana lissafin rijiyoyin sai da aka daina domin abin ya fi gaban tunani. Kai a karshe ma sai da ya rinka kyautar durhami dare da sana ga fadawansa da talakawan gari kullum dare da rana domin bashi da inda zai ajiye kudin.
Kusan a kowanne karshen shekara fadawansa masu yi masa fatauci mutum dubu arba'in ne suke kawo ribar kudi ta miliyoyin dirhamomi.
Shi kansa Sarki Maharaz akwai lokacin da ya dubi gunkin Darbuza ya ce da shi, "Dukiyar da kake bani ta isheni rayuwa har mutuwata, kai tattaba kunnena ma ba za su yi talauci ba, don haka a daina bani kudi haka!"
A duk sa'adda Sarki Maharaz yayi wannan furuci ga gunki Darbuza sai yaji ya tuntsire da dariya, sannan ya ce da shi, "Ba zamu daina zubo maka kudi ba daga nan har bayan mutuwarka sabo da idan muka daina baka wani zai iya tasowa ya fika, mu kuwa burinmu shi ne ka ci gaba da shara ya zamana cewa a zamaninka ba a sami sa'anka ba."
Koda jin haka sai farin ciki ya baibaye Sarki Maharaz ya yi godiya sannan ya mike ya fita daga dakin bautar gunkin Darbuza.