Ya masoyina ka Sani rayuwa babu kai, bata da amfani tamkar mota ce babu mai,Kai nake buri kuma nake muradi a ko da yaushe, Ka Sani ina yinka.!!!
Ya sinadarin da ke tada min da kaikayin tsokar zuciya ta, kai daya ne tamkar dubu a wajena, ka kauda duk wata shakka, ina sonka!
Ya habibi ka zamto ruwan idaniya ta, bana zubar da hawaye ne kadai don kada na rasaka,,,,ka sani cewa bana sha'war komai sai jin muryar ka, bana iya ko cin abinci sai naga fuskarka!
Ya masoyi, ka sani cewa a kullum da kai nake kwana, haka nan da kai nake tashi, soyayyarmu kuwa ko a tari ba za'a kamar ta ba!
Ina farin cikin sanar da saurayi mai farin doki, mai fararen hakora, mai farin aninya, cewa "INA SONKA" kuma, ba wacce ta isa ta rabani da kai sai mutuwa!
Harshe bata isa ta fadi adadin son da nake maka ba, fuska bata isa ta nuna adadin farin cikin da ka sanyani a cikin ta ba, ina kaunarka!
Duk mai son ya koyi gina Website hadaddiya to maza ya hadu da mu a dandalin mu na koyarwa a facebook SHIGA
Ana iya turo mana da sakonni na Comment (Turo) ko ka shiga dakin Muhawara don tambaya, ko korafi (Shiga)