Assalamu alaikum ya Rabin raina (suna) ,ki sani rabuwar mu ba alheri bane ,tamkar rabuwar da da uwa ne ko kuwa rabuwar kai da gangan jiki.Sai dana koma gida a tunanina zan iya jurewa,,kash amma sai naji bana sha'awar wata mace sai ke!.Ina mai durkusa wa gare ki ,ki yafe ni! Share
Masoyiya ta a duk lokacin da naji muryar ki
nakan samu natsuwa a zuciya ta,
Murmushin ki gare ni yafi aban kyautar
sabuwar mota da gida.
Fuskar ki a kullum haske take kara yi
musamman idan kina murmushi, Idan kika yi
fushi sannan ne kike dada kara kyan gani amma bana nufin in bata miki!
Ya alawar zuciya ta, ni dai a duniyan nan ban ga wacce ta kai ki ba, dan Allah masoyiya ki bani dama na furta miki soyayya ta!
A yau ne na tabbatar nayi gamo, gamo da wacce zata sharen hawaye na, gamo da wacce zata zamo uwar 'ya'ya na, gamo da wacce zata kasance tare dani koda za'a guje ni ,Ina Sonki!
Ya halwar dake sanyaya zuciyar masoyi, ya kankarar dake daskarar da bakin cikin zuciyar masoyi, kiyi min rai, kiyi min gafara, ki sani ni dai ina kaunarki!
Kece AC dake sanyaya cikin ruhina.. Ki zama subsidat na zama subsideen, mu hadu mu dawo da tallafin kauna a Nigeria!!
Shin baki sani ba masoyiya wallahi a shirye nake na shanye dukkanin duka saboda ke,kin zama Rabin jikina, kuma ki sani rayuwa babu ke tamkar bindiga ne babu harsashi!
Ya gimbiya ta wai shin akwai abin da zai raba mu kuwa bacin mutuwa? Ya kamata mu hade kammu don kar makiya su cimma mana.
Ya masoyiyata, ki zamo bishiya in zamo
ruwan da zai ratsa ta kasarsa ba dan kome
ba sai dan in shayar da ke.
Ya masoyiyata, ki zamo hanta in zamo jini,
muga mai raba mu.
Ludayin kaunar ki ya mamaye min kokon
zuciyata.
Ya masoyiyata, ki zamo mai in zamo alabasa
mu hadu mu soye juna.
Duk mai son ya koyi gina Website hadaddiya to maza ya hadu da mu a dandalin mu na koyarwa a facebook SHIGA
Ana iya turo mana da sakonni na Comment (Turo) ko ka shiga dakin Muhawara don tambaya, ko korafi (Shiga)