Old school Swatch Watches
bahaushe logo
DAKIN BARKWANCI

BARKWANCI NA NUFIN BA'A KO WASA A TSAKANIN WASU KABILU KO RUKUNIN AL-UMMA MASU ALAKA TA AL-ADA KO ZAMANTAKEWA DON TUNZURA JUNA BA TARE DA SAMUN SABANI A TSAKANINSU BA.

KALMOMI DA DA ZASU IYA DAUKAR MA'ANAR BARKWANCI SUN KUNSHI,WASA,NISHADI,ZOLAYA,RAHA DA SAURANSU.

SAURAYI DA BUDURWA
Wani Bakatsine ya je hira wajen budurwarsa, bayan sun gama zai tafi sai ya sa hannu a aljihu ya dauko kudi ya ba ta. Sai budurwar ta ce ba za ta karba ba. Shi kuma ya ce:“To tun da ba ki so, ni ma ba na so.” Sai ya yi watsi da kudin a nan, kowa ya kama gabansa. To ashe ita wannan budurwa ba tafiya ta yi ba, ta dan labe ne a wani waje a gidan, da niyyar idan saurayin ya tafi ta zo ta kwashe kudin. Haka shi ma Bakatsine bai tafi ba, ya dan labe a kofar gidan da niyyar idan yarinyar ta shiga gidan ya zo ya kwashe kudinsa. To dama a cikin soro suke zancen kuma an dauke wuta, can sai saurayin da budurwar suka dawo cikin soron, suka fara laluben kudin ba tare da kowannensu ya ga dan uwansa ba. Can sai aka kawo wuta, nan take sai Bakatsine ya wayance ya ce wa budurwar: “Don Allah ba ki ga wayata ba?” Ita ma budurwar ta ce masa: “Ni ma don Allah ba ka ga sarkata ba?
GA LAMBA TA
Wata rana wani bahaushe ya hadu da wata Bayarabiya wai sonta yake yi, Har ya tambaye ta lambar waya, SAI TACE "WRITE :-SERO HATE SERO, SIS HATE SIS, SEFUN SEFUN TO TERE HON (0806867231)" Dariya ya subuce wa gogan naka, DAGA CAN YACE GA LAMBATA "RUBUTA:- TZIRO SABUN TZIRO TIRI SIS PIPE PIPE WAN POR ELABUN (07036551411)" BAYARABIYA TA TINSIRE DA DARIYA!
WUTA MUKA JABA
Wani Bafulatani ne sanyi ta dame shi ,a lokacin an gama kwaza ruwan sama , sai ya hada wuta yana jin dumi, kai ko da wuta ta ratsa gogan nan naka sai ya budi baki ya ce : "HANDE WALLAHI KO A LAHIRA WUTA MUKA JABA"
HANCIN WAYE
Wata mota ce tayi hadari a hanyarta ta tafiya, bayan wa su sun dawo hayyacin su ,sai dayansu ya tsinci hanci a kasa, ya dauka ya fara zagawa yana tambaya "Wa hancinsa ya fadi?" da ya gaji yayi zufa sai ya ja tsaki Mtsssw.Ya sa sa hannu don ya share zufa kawai sai ya ji ba hanci a fuskarsa , sai ya bushe da dariya, daga nan ya fara zagin direba
CARY OVER
WANI MALAMI MAI HANNU DAYA YANA KOYAR DA HARSHEN HAUSA, RANNAN YAYI LECTURE AKAN "KARIN MAGANA" DAGA KARSHE YACE KOWA YA KAWO MISALI DAYA, WATA BUDURWA TA TASHI TACE:- KO BA A GWADA BA HANNU DAYA BAI DAUKAR JINKA (KOWA YAYI DARIYA) MALAMIN YACE AMMA NA BADA CARY OVER AI DAN UBANKI!"
NA SHANYA YA BUSHE
Wasu mahaukata biyu suna zauna a kan sokawe ,can sai karamin ya zurmuke ciki,Babban ya tashi yayi yekuwa a "kawo agaji",kafin a taru gogan naku yayi zuciya ya shiga ya ciro dan'uwansa, kana ya shige dashi cikin gida.
Can anjima ya fito yayi arba da mutane suna jiran tsammani, me ya faru? ina dan'uwanka? Gogan naku yace ha ha ha ya fadi a sokawe yanzu na cire kuma na shanya shi ya bushe, koda aka shiga sai aka iske shi a rataye a jikin fanka na kakarin mutuwa!
KOWA ZAI SAMU
Wani mahaukaci yana gasa mushen kyanwa,sai yara suka taru har da ture-ture ana kallo, gogan naka daya ga sai yace inkunyi hakuri "KOWA ZAI SAMU"
Idan shafinnan ya burge ka, Mai zai hana ka sharin namu a group na abokanka
Bahaushe is loading comments...
Duk mai son ya koyi gina Website hadaddiya to maza ya hadu da mu a dandalin mu na koyarwa a facebook SHIGA
Ana iya turo mana da sakonni na Comment (Turo) ko ka shiga dakin Muhawara don tambaya, ko korafi (Shiga)
| | | | |
Online counter:  free web counter Counter Powered by  RedCounter
engTranslate This page
Kirkira:
Umar Muhammad Bappa Plateau state. NIGERIA
© Bahaushe 2016