Teya Salat
bahaushe logo
KUNDIN SOYAYYA
SHIN MENENE SO ?

So wata sinadari ce wacce take shiga zuciyan mutum lokacin guda da ganin abu kuma ya kamu da son abun, a hakan baya cika soyayya har sai yaji yana sha'awar abun sosai kuma yana begen abun sosai!

MENENE KAUNA ?

Bayan mutum ya kamu da son abun, akwai bukatun tabbatar da so ta gaskiya da jaddadata tsakani da Allah,sannan kuma ya kudira niyyar komai rintsi bazai rabu da wannan abinda yake so ba! Wannan shi ne KAUNA!

KALAMAN SO GA MATA
Assalamu alaikum ya Rabin raina (suna) ,ki sani rabuwar mu ba alheri bane ,tamkar rabuwar da da uwa ne ko kuwa rabuwar kai da gangan jiki.Sai dana koma gida a tunanina zan iya jurewa,,kash amma sai naji bana sha'awar wata mace sai ke!.Ina mai durkusa wa gare ki ,ki yafe ni!
Ya abar qaunata, ke kadai ke iya kwantar da tarzomar zanga-zangar soyayya a cikin zuciyita Ya ranar da ke haske duniyar zuciyata, ki zamo nono in zamo fura mu hade a kwaryar qauna, a dame mu da ludayin soyayya.
KALAMAN SO GA MAZA
Ya masoyina ka Sani rayuwa babu kai, bata da amfani tamkar mota ce babu mai,Kai nake buri kuma nake muradi a ko da yaushe, Ka Sani ina yinka.!!!
Ya habibi ka zamto ruwan idaniya ta, bana zubar da hawaye ne kadai don kada na rasaka,,,,ka sani cewa bana sha'war komai sai jin muryar ka, bana iya ko cin abinci sai naga fuskarka!
ABIN MAMAKI A SOYAYYA
Kashi 70(saba'in) na yammatan zamani suna son maza ne don dukiyar su!
Kashi 70 cikin maza kuwa don kyawun mace (launin farin fata) kawai suke sonsu!
Masu cewa in na rasa ki a rayuwa ba zan rayu ba a maza 10% ne kawai za su iya sauran kuma suk cika baki suke!
A cikin mata kuwa masu cewa "In na rasa ka a rayuwa zan sheke nima "30% ne zasu iya a cikin dari!
Duk mai son ya koyi gina Website hadaddiya to maza ya hadu da mu a dandalin mu na koyarwa a facebook SHIGA
Ana iya turo mana da sakonni na Comment (Turo) ko ka shiga dakin Muhawara don tambaya, ko korafi (Shiga)
| | | | |
Online counter:  free web counter Counter Powered by  RedCounter
engTranslate This page
Kirkira:
Umar Muhammad Bappa Plateau state. NIGERIA
© Bahaushe 2016